Dan Kamaru N'Koulou ya koma Marseille

nkoulou Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nicolas N'Koulou na Kamaru

Dan kwallon Kamaru Nicolas N'Koulou ya kulla yarjejeniyar shekaru hudu da Marseille daga kungiyar Monaco.

Rahotanni sun nuna cewar an cefanar da dan kwallon ne akan dala miliyan biyar.

A cikin yarjejeniyar, Marseille ta baiwa Monaco aron dan kwallonta na kasar Togo Senah Mango.

N'Koulou mai shekaru 21 zai hade a Marseille tare da takwaransa na Kamaru Stephane Mbia wanda suke kare bayan tawagar Indomitable Lions.

Marseille ce zakaran gasar Faransa a shekara ta 2010 amma a bara Lille ce ta lashe gasar.

A halin yanzu dai Taye Taiwo da Gabriel Heinze sun fice daga kulob din.

Har wa yau Marseille na gabda kulla yarjejeniya da dan wasan Faransa Alou Diarra daga Bordeaux.