Sunderland na gab da sayen Wickham daga Ipswich

Connor Wickham
Image caption Wickham ya fara taka wa Ipswich leda tun yana shekara 16

BBC ta fahimci cewa Ipswich ta amince da tayin Sunderland na fan miliyan 9 domin sayen dan wasan gaban Ipswich din Connor Wickham.

Wickham mai shekaru 18, zai zamo dan wasan Sunderland da zarar ya cimma yarjejeniya tsakaninsa da su, sannan kuma an gwada lafiyarsa.

Gaba daya dai cinikin zai kai fan miliyan 12 da rabi - dan wasan dai yana bugawa tawagar Ingila ne ta 'yan kasa da shekaru 21.

A baya an danganta shi da kungiyoyi da dama a Premier ciki harda Tottenham da Liverpool.

Dama an dade ana nuna shakku kan makomarsa duk da cewa ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragin da za ta bashi damar ci gaba da zama a Ipswich har zuwa shekara ta 2014.