Kada ku duba shekarun Villas-Boas-Cech

peter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Petr Cech

Golan Chelsea Petr Cech ya bayyana cewar kada a duba shekarun sabon kocin kulob din Andre Villas-Boas amma a duba irin ayyukan da zai yi.

Villas-Boas mai shekaru 33 yafi Cech ne da shekaru hudu kuma ya bar Porto zuwa Stamford Bridge a watan Yuni.

Cech yace"idan dan kwallo nada shekaru 16 kuma ya isa ya taka leda cikin manya, to haka lamarin yake akan batun koci".

Ya kara da cewar tunda Villas Boas ya lashe gasar Europa a kakar 2010/11, ya nuna cewar shi gwani ne.

A cewar Cech bai riga ya tattauna da sabon kocin ba amma ya sanshi lokacin yana aiki karkashi Mourinho.

Cech ya jadadda cewar ba zai dauki 'yan kwallon lokaci mai tsawo ba kafin su gane irin salon Villas-Boas.