Dambe:Wladimir Klitschko ya casa Haye

Wladimir Klitschko ya doke David Haye Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wladimir Klitschko ya doke David Haye

Wladimir Klitschko ya doke David Haye a dambe nauyi mafi girma a duniya a karawar da suka yi ranar Asabar a Hamburg.

Sun kara ne a gaban 'yan kallo dubu 45 daga cikinsu dubu 10 'yan Birtaniya ne, amma kuma an nunawa Haye ruwa ba tsaran kwando bane a wasan daya kaisu har zagaye na 12.

Haye ya yi alkawarin fidda sabuwar dabara ta fada amma kuma sai Klitschko dan Ukraine ya casa shi.

Alkalai uku duk sun baiwa Klitschko nasara inda suka bada maki kamar haka:117-109, 118-108 da 116-110.

Wannan ne karo na farko da aka doke Haye, tun bayan kashin daya sha a wajen Carl Thompson a damben matsakaicin mataki a shekara ta 2004.

Kenan a yanzu cikin karawar 25, an samu galaba akan Haye sau biyu a yayinda shi kuma Klitschko ba a kara doke shi tun shekara ta 2004, kuma ya samu nasara 56 da kuma casa shi sau uku.