Dan Kamaru N'Guemo ya koma Bordeaux

ngueomo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan Kamaru Landry N'Guemo.

Kungiyar Bordeaux ta Faransa ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Kamaru Landry N'Guemo.

N'Guemo ya koma Bordeaux ne bayan kwangilarsa ta kare a Nancy.

A ranar Litinin ne dan kwallon mai shekaru 25 za a gabatar dashi gaban magoya bayan kulob din, bayan ya sanya hannu a kwangilar shekaru uku.

Kungiyar Buraspor ta Turkiya ta nuna sha'awarta akan dan Kamarun, amma sai kocin Bordeaux Francis Gillot ya shawo kansa.

N'Guemo yace"Na tattauna da kocin kulob din kafin in amince da kwangilar".

Dan wasan na cikin tawagar Indomitable Lions a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010.