Saudi Arabia ta nada Rijkaard a matsayin koci

ijkaard
Image caption Frank Rijkaard

Saudi Arabia ta nada tsohon kocin Netherlands da Barcelona Frank Rijkaard a matsayin mai horadda 'yan kwallonta.

Tsohon kyaftin din Ajax Amsterdam ya kulla yarjejeniyar shekaru uku da Saudiya kamar yadda hukumar kwallon nahiyar Asiya ta wallafa a shafinta na Intanet.

A baya Saudi Arabia tayi niyyar nada dan Brazil Ricardo Gomes a matsayin koci, amma sai suka samu rashin jituwa akan batun ranar da zai fara aiki.

A watan Oktoban bara ne Rijkaard mai shekaru 48 ya bar kungiyar Galatasaray ta Turkiya.

Babban aikin dake gaban sabon kocin shine ya tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin duniya a Brazil na shekara ta 2014.