2013:Algeria na son ta maye gurbin Libya

CAF
Image caption A watan Satumba CAF zata yanke hukunci akan Libya

Algeria ta hade da Afrika ta Kudu wajen nuna sha'awarta na daukar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a 2013.

Bisa tsari dai Libya ce ya kamata ta dauki bakuncin gasar amma saboda tashin hankalin dake gudana a kasar ya janyo hukumar CAF na tunanin canza inda za ayi a gasar.

A watan Satumba ne hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF zata yanke hukunci akan ko za a bar Libya ta dauki bakuncin gasar ko kuma a baiwa wata kasar dama.

Afrika ta Kudu ce zata dauki bakuncin gasar a 2017, kuma tuni ta bayyana aniyarta na maye gurbin Libya idan hakan zai yiwu.

Za ayi gasar kwallon kasashen Afrika a badi a kasashen Equatorial Guinea da Gabon.

A baya dai Afrika ta Kudu ta maye gurbin Libya wajen daukar bakuncin gasar matasan Afrika sakamakon fara tashin hankali.