Diarra ya koma Marseille daga Bordeaux

Alou Diarra Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alou Diarra

Dan kwallon tsakiyar Faransa Alou Diarra ya kamalla kulla yarjejeniya da Bordeaux daga kulob din Marseille.

Rahotanni sun nuna cewar ya kulla yarjejeniyar shekaru uku akan Euro miliyan hudu da rabi.

Dan kwallon mai shekaru 29 ya dade a cikin jerin 'yan wasan da kocin Marsielle Didier Deschamps ke zawarcinsa.

A baya ya taka leda a Bayern Munich da Liverpool da kuma Lyon kuma yana cikin kashin bayan tawagar Bordeaux data lashe gasar kwallon Faransa dana FA a shekara ta 2009.

Ya bugawa Faransa kwalloa karon farko a shekara ta 2004 kuma ya taka leda a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006.