Zamu dakatar masu joge a wasa-Blatter

blatter
Image caption Sepp Blatter

Shugaban Fifa Sepp Blatter yace duk wanda aka kama da laifin sayarda wasa ko joge a harkar kwallon Zimbabwe za a dakatar dashi na muddin rai.

Manyan 'yan wasan kasar hadda kyaftin din tawagar Method Mwanjali ya bayyana cewar an basu kudi don su bari a dokesu a wata gasa a shekara ta 2009.

Jami'an Fifa masu yaki da rashawa zasu ziyarci Zimbabwe don tattaunawa da jami'an kwallon kasar da 'yan sanda don kamalla binciken lamarin.

Blatter ya bayyana haka ne a ziyararsa a Harare ya kara da cewar" ba zamu shiga cikin lamarin ba a matakin farko, zamu bar hukumomin tsaro suyi aikinsu a kasashe daban daban kuma idan aka kama su da laifi za a dakatar dasu muddin rai".

'Yan kwallon Zimbabwe sun bayyana cewar jami'ai sun yi aiki da wani dan kasar Singapore Wilson Raj Perumal don su sha kashi tsakaninsu da Syria da Thailand.