Pedro ya sabunta kwangilarsa a Barcelona

rodriguez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pedro Rodriguez

Dan kwallon Spain Pedro Rodriguez ya sabunta yarjejeniyarsa da Barcelona har zuwa shekara ta 2016.

Sanarwa da Barcelona ta fitar ta ce "Mun kulla yarjejeniya da Pedro Rodriguez inda ya kara shekara guda a kwangilarsa har zuwa 30 ga watan Yuni na 2016".

Pedro mai shekaru 23 na cikin tawagar Spain data lashe gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihinta a shekara ta 2010.

Yana daga cikin zaratan 'yan wasan Barca tare da Lionel Messi da David Villa da suka lashe gasar zakarun Turai a bana sannan ya ci kwallaye 22 a kakar wasan data wuce.