Arsenal sai kyale-kyale babu tasiri-Scholes

scholes
Image caption Paul Scholes

Tsohon dan kwallon Manchester United Paul Scholes ya karawa Arsenal gishiri a ciwo, inda ya zarge ta da yin kyale-kyale amma babu tasiri.

Da yake jawabi kafin bukin karramashi da za ayi a Old Trafford a wata mai zuwa, Scholes ya ce babu yadda kocin United Sir Alex Ferguson ya bari kulob din ya shafe shekaru shida babu kofi kamar yadda lamarin yake a Arsenal. Scholes yace"watakila suke taka leda me ban sha'awa amma kuma babu sakamako me kyau".

Scholes yana cikin hammayar United da Arsenal cikin shekaru goma da suka wuce, ya kuma zargi kocin Arsenal Arsene Wenger a kakar wasan data wuce wai yana cikin mawuyacin hali a tarihinsa na kwallo.

Wasan karshe da Scholes ya bugwa United shine na gasar zakarun Turai da Barcelona ta lashe a filin Wembley.