Chelsea zata nada Emenalo darektan wasanni

Michael Emenalo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Michael Emenalo

Tsohon dan kwallon Najeriya Michael Emenalo na gabda zamowa sabon darektan kula da wasanni na kungiyar Chelsea ta Ingila.

Dan shekaru 45, tsohon dan wasan Super Eagles din zai maye gurbin Frank Arnesen wanda ya karbi irin mukamin a kungiyar Hamburg ta Jamus.

Emenalo ya hade da kulob din a shekara ta 2007 a matsayin mai farautar 'yan wasa sannan aka mai dashi mataimakin koci sakamakon tafiyar Ray Wilkins a watan Nuwamban bara.

Ya bugawa Najeriya gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.

A baya ya taba taka leda a Notts County, da kuma wasu kulob a Amurka da Spain da Jamus da kuma Isra'ila.

Emenalo zai yi aiki tare da sabon kocin Chelsea Andre Villas-Boas.