Hammam na gabda sannin makomarsa a Fifa

hammam
Image caption Mohammed Bin Hammam

Kwamitin da'a na Fifa zai tattauna a ranar 22 da 23 ga watan Yuli don sauraron ba'asi akan Mohammed bin Hammam wanda aka dakatar bisa zargin cin hanci da rashawa.

Hammam dai zai kare kansa akan batun zargin sayen kuri'u don baiwa Qatar damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022.

An kamalla bincike kuma an aika rahoton ga shugaban kwallon nahiyar Asiya Bin Hammam wanda aka dakatar.

Jami'an kwallon Caribbean Debbie Minguell da Jason Sylvester suma zasu gurfana gaban kwamitin.

Minguell da Sylvester an dakatar dasu tare da mataimakin shugaban Fifa Jack Warner wanda aka dakatar da bincike akansa sakamakon murabus daga harkar kwallon kafa a duniya.

Abinda ake bincike nada nasaba da batun taron kungiyoyi 25 da aka yi a watan Mayu, inda aka yi zargin ambada cin hancin dala dubu arba'in don su zabi Bin Hammam, wanda a lokacin yake takarar shugabancin Fifa.