Zidane zai zama darekta a Real Madrid

zidane
Image caption Zinedine Zidane

Zinedine Zidane zai fara aiki a matsayin darektan kwallon kafa na Real Madrid a mako mai zuwa.

Tsohon gwarzon dan kwallon duniya din mai shekaru talatin da tara a yanzu shine me baiwa shugaban Real Florentino Perez shawara.

Zidane yace"zamu fara aiki a matsayin darekta kwallon kafa kuma Mourinho ke ya kulla abin".

Zidane zai dauki ayyukan dda a baya Jorge Valdano ke yi kafin a koreshi a matsayin darekta Janar.

Rashin jituwa tsakanin Valdano da Mourinho ya yi kamari ne abinda kuma ya sanya Perez ya sallami Valdano don barin Mourinho yayi aiki babu takura.

Zidane ya taikama kawa Real ta lashe gasar zakarun Turai a shekara ta 2002 a wasan karshe tsakaninta da Bayer Leverkusen.

Yayi ritaya daga kwallo bayan shafe shekaru biyar tare da Real a shekara ta 2006.