Ghana na taya Essien juyayi akan rauni

essien
Image caption Micheal Essien ya koma Chelsea a 2005

Hukumar kwallon Ghana ta nuna damuwarta akan raunin da Micheal Essien ya samu.

Dan kwallon Chelsea da Black Stars din ya jimu a Ingila a cikin mako daya gabata a gwiwarsa ta dama lokacin yana horo.

Gwajin da aka gudanar ya nuna cewar dan wasan ya ji matsanancin rauni.

Sanarwa da GFA ta fitar ta ce"GFA da daukacin 'yan kasar Ghana na yiwa Micheal Essien jaje wannan yanayin daya samu kansa a ciki da fatar cewa ba zai dade yana jinya ba".

Dan kwallon mai shekaru 28 ya jinyar fiye da watanni shida a shekara ta 2008 lokaci da raunata.

Essien har wa yau bai buga gasar cin kofin duniya ba a shekara ta 2010 saboda rauni a gwiwarsa.

Jimuwar da Essien yayi ba karamin cikas bane ga sabon kocin Chelsea Andre Villas-Boas wanda ke shirye shirye tafiya nahiyar Asiya don buga gasar Asian Cup.

Essien ya koma Blues da kulob din Lyon a shekara ta 2005 akan fan miliyon 24.4 kuma ya kasance daya daga cikin manyan 'yan wasan Stamford Bridge.