Qatar 2022:Jami'ar data yi zargi ta janye

qatar Hakkin mallakar hoto None
Image caption Qatar ta doke Amurka don samun damar

Wata jami'a wacce tayi zargin cewar Qatar ta baiwa mambobin Fifa uku cin hanci don kasar ta samu damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022, ta ce karya tayi.

Phaedra Al Majid wacce tayi aiki a matsayin jami'ar yada labarai na Qatar 2022 ta shaidawa BBC cewar tayi ramuwar gayya ne bayan an koreta a aikinta don ya batawa Qatar dib suna sai ta kago labarin.

Al Majid ta sanya hannu a wata takardar kotu na janye maganar kuma ta ce ba matsin lamba bace ta sanya ta janye zargin.

Tace"Na shiga damuwa don an koreni sai nayi ramuwar gayya".

Al Majid a lokacin ta zarge 'yan Afrika uku Issa Hayatou da Jacques Anomua da kuma Amos Adamu wanda aka dakatar akan cewar saida aka biyasu suka zabi Qatar.

Duk su ukun sun karyata zargin.