Arsenal ta sayi Gervinho daga Lille

gervinho
Image caption Gervinho

Arsenal ta tabbatar da sayen dan kwallon Ivory Coast Gervinho daga kungiyar Lille .

Dan kwallon mai shekaru 24 ya zira kwallaye 15 da suka taimakawa Lille ta lashe kofina biyu a Faransa a kakar wasan data wuce.

Gunners a yanzu sun tafi rangadi zuwa yankin gabashin Asiya kuma manajan kulob din Arsene Wenger ya ce"Gervinho ya hade damu,kuma an gwada lafiyarsa a ranar Alhamis".

Gervinho wanda ya jagoranci Ivory Coast zuwa gasar Olympics a Beijing a shekara ta 2008 ya bayyana cewar ya zabi Arsenal ne saboda tawaga ce mai matasan 'yan kwallo.

Jerin 'yan kasar Ivory Coast dake taka leda a gasar premier ta Ingila:

* Emmanuel Eboue, Arsenal * Gervinho, Arsenal * Didier Drogba, Chelsea * Salomon Kalou, Chelsea * Abdul Razak, Man City * Kolo Toure, Man City * Yaya Toure, Man City * Cheik Ismael Tiote, Newcastle * Abdoulaye Meite, WBA * Steve Gohouri, Wigan