Wolves na gabda sayen Johnson daga Birmingham

johnson
Image caption Roger Johnson

Wolverhampton Wanderers na gabda kulla yarjejeniya da dan kwallon Birmingham City Roger Johnson bayan kungiyoyin biyu sun amince akan fan miliyon bakwai.

Rahotanni sun nuna cewar dan kwallon mai shekaru 28 zai koma Wolves dinne don kara karfin tawagar a baya.

An dade ana bayyana cewar Johnson zai bar Birmingham tun lokacin da kulob din ya premier ta koma Championship.

Yarjejeniyar zata yi dai dai da cinikin da yafi kowanne tsada a Wolves lokacin da aka sayi Steven Fletcher.

Manajan Wolves Mick McCarthy yayi zawarcin dan kwallon Reading Matt Mills amma sai aka ki amincewa da tayin fan miliyon uku da Wolves tayi.

Johnson ya koma St Andrew daga Cardiff a shekara ta 2009 a kwangilar shekaru uku.

Johnson ya bugawa Birmingham wasanni 88 inda ya zira kwallaye uku kuma yana cikin tawagar data lashe kofin Carling.