Woodgate ya kulla yarjejeniya da Stoke City

Jonathan Woodgate Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jonathan Woodgate

Dan kwallon Tottenham Jonathan Woodgate ya kulla yarjejeniya da Stoke City.

Tsohon dan kwallon Ingila mai shekaru 31 ya amince ya bugawa Stoke City kwallo a yarjejeniyar da sai ya buga kwallo za a biya shi.

Kocin Stoke Tony Pulis yace"mun san cewar wasu kulob din premier sunyi zawarcinsa amma kuma mune muka same shi".

Woodgate na daya daga cikin 'yan kwallon Ingila da ya dade yana jinya abinda ya kawo masa tsaiko a rayuwar kwallonsa.

Ya bugawa Leeds a shekarar 1998 yana kuma cikin tawagar data kai wasan zagayen kusada karshe na gasar zakarun Turai a shekara ta 2001.

Woodgate ya taba bugawa Newcastle da Real Madrid da Middlesbrough da kuma Tottenham