'Yan kwallon Eritrea 13 sun yi layar zana

eritrea
Image caption Taswirar kasar Eritrea

'Yan kwallo goma sha uku daga cikin tawagar 'yan wasan Eritrea sun ki komawa gida bayan kammala gasar yanki a kasar Tanzania.

Bayan da kulob din Red Sea FC ya sha kashi a wasan zagayen kusada karshe a ranar Asabar, rabin tawagar ne kadai suka je filin jirgin sama don komawa gida Eritrea.

Wannan ne karo na hudu da 'yan kwallon Eritrea ke yin batar dabo.

Matasa a Eritrea kan gojewa kasar don kaucewa talauci da gwamnatin kama karya na soji.

Jami'in hukumar kwallon Tanzania Angetile Osiah ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar an kai karar batun layar zanan zuwa hukumomin tsaro don gudanar da bincike.