Ramos da Pepe sun sabunta kwangilarsu da Real

ramos Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Sergio Ramos na gurmuzu da Lionel Messi a gasar La Liga

Real Madrid ta sanarda cewar 'yan kwallonta biyu Sergio Ramos da Pepe sun sabunta yarjejeniyarsu na shafe lokaci mai tsawo da kulob din.

Sanarwar da Real ta fitar ta ce "Sergio Ramos da Pepe sun sabunta kwangilarsu don kasancewa da Real Madrid zuwa shekara ta 2017 da kuma 2016".

Ba a samarda cikakkun bayanai akan yadda sabuwar kwangilar take.

Pepe dan kasar Portugal rahotanni sun nuna cewar za a dinga biyanshi akalla dala miliyon biyar da dubu dari shida a kowacce shekara.

A bangaren Ramos kuwa, kwangilarsa ta kai akalla dala miliyon shida da dubu dari uku.