Man City ta maidawa Wenger martani

city Hakkin mallakar hoto
Image caption Filin wasa na Manchester City

Manchester City tayi watsi da kalaman Arsene Wenger akan batun sabuwar yarjejeniyar sake sunan Eastlands, inda Wenger yace yarjejeniyar ta sabawa dokar kudi ta Uefa.

Kocin Arsenal ya ce yarjejeniyar zata lakume makudan kudade tsakanin City da kamfanin Etihad Airways.

Sabuwar dokar ta ce kulob kulob basu kashe fiye da abinda suke samu,kuma harajin da ake samu yazo dai dai da darajar kasuwa.

City ta bayyana kalaman Wenger a matsayin "babu makama babu tushe".

A makon daya gabata ne City ta bada sanarwar canza sunan Eastlands ya koma 'Etihad Stadium' a wata yarjejeniyar da zata sanya kudaden shigar City ya kai kusan fan miliyon 400.