Queens Park Rangers ta sayi Kieron Dyer

Kieron Dyer. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kieron Dyer

Queens Park Rangers ta kamalla kulla yarjejeniya da Kieron Dyer.

Dan kwallon mai shekaru 32, a karshen kakar wasan data wuce ya bar West Ham, kuma a yanzu ya hade da QPR a kwangilar shekara guda.

Dyer ya bayyana cewar"Naji dadin kasancewa a nan".

Dyer ya koma West Ham daga Newcastle United a watan Agustan 2007 akan fan miliyon shida amma wasanni 34 kacal ya buga saboda rauni.

Sannan kuma an bada shi aro na wata guda zuwa Ipswich Town a kakar wasan data wuce.

Ya soma buga kwallo a matakin kwarare a shekarar 1996 tare da kungiyar Suffolk kafin ya koma Newcastle.