Boateng na gabda komawa Bayern daga City

Jerome Boateng Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jerome Boateng

Dan wasan Manchester City Jerome Boateng na kan hanyarsa ta komawa Bayern Munich a yarjejeniyar shekaru hudu.

Dan shekaru ashirin da biyu wanda ya koma City ne daga Hamburg a shekara ta 2010.

Dan wasan Jamus din, Boateng din zai koma Munich akan kudin da ba a bayyana ba, kuma za a gwada lafiyarsa a kwanaki masu zuwa.

Shugaban Bayern Karl-Heinz Rummenigge yace: "Bayan sasantawa mai tsawo a yanzu mun samu nasarar kammala yarjejeniyar".

Shi kuwa darektan wasanni a Bayern Christian Nerlinger cewa yayi "Matashin dan kwallo ne kuma zai yi dai dai da tsarin FC Bayern".

Bayan nasarar daya samu a gasar cin kofin duniya da aka yi a Afrika ta Kudu a bara, dan kwallon Jamus din ya kulla yarjejeniya da City amma kuma saboda fama da rauni, wasanni 24 kacal ya bugawa kulob din a kakar wasam data wuce.