Aston Villa na zawarcin N'Zogbia

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Charles N'zogbia yana taka leda a wasan da Wigan ta buga da West Ham a kakar wasan bara

Aston Villa na zawarcin dan wasan Wigan Athletic Charles N'Zogbia.

Sabon kocin kungiyar Alex McLeish, yana neman dan wasan da zai maye gurbin Stewart Downing, wanda ke shirin komawa kungiyar Liverpool.

Villa dai ta siyarwa Manchester United dan wasanta Ashley Young a watan daya gabata.

N'Zogbia mai shekarun haihuwa 25, ya taka leda a gasar Premier ta Ingila sau 250, a kungiyar Wigan da kuma tsohuwar kungiyarsa ta Newcastle.