Boateng ya koma Bayern akan fan miliyon 15

jerome Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jerome Boateng

Dan kwallon baya na Manchester City Jerome Boateng ya kammala kulla yarjejeniyar shekaru hudu da Bayern Munich.

Rahotanni sun nuna cewar Boateng ya koma Bayern ne akan kusan fan miliyon 15.

Boateng ya koma City ne daga Hamburg akan fan miliyon goma a shekara ta 2010 amma kuma bai samu damar taka leda sosai ba a kulob din.

A makon daya gabata ne dan kwallon Jamus din ya fice daga rangadin da Manchester City keyi a yankin Arewacin Amurka dun ya kammala sansantawa da Bayern.

Wasanshi na karshe a City shine a ranar biyu ga watan Maris a wasan gasar kofin FA tsakaninta da Aston Villa.

Sabon kocin Bayern Jupp Heynckes ya bayyana cewar"Na samu labari me kyau akan Boateng kuma yayi dai dai da tsarin horonmu".