Man City ta amince da tayin da aka yiwa Tevez

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Carlos Tevez

Kocin Manchester City, Roberto Mancini ya ce kungiyar ta amince da tayin da kungiyar Corinthians ta yiwa dan wasan ta Carlos Tevez.

A makon daya gabata ne dai City ta ki amincewa da tayin fam miliyan 39 da kungiyar Corinthians ta yi akan dan wasan, a yayinda rahotanni suka yi nuni da cewa City na neman fam miliyan 50 ne akan dan wasan.

Tevez, mai shekarun haihuwa 27, ya ce yana so ya bar gasar Premier domin kasarsa ta haihuwa wato Argentina, inda yake ganin zai fi samun lokacin kula da iyalinsa.

"Mun cimma yarjejeniya da Corinthians amma har yanzu Carlos dan wasan mu ne." In ji Mancini