Aston Villa na gabda sayen Given daga City

given
Image caption Shay Given

Aston Villa na gabda kamalla kulla yarjejeniyar fan miliyon uku da rabi akan golan Manchester City na kasar Ireland Shay Given.

Sabon kocin Villa Alex McLeish ya koma kan golan mai shekaru 35 bayan Brad Friedel ya koma Tottenham.

A yanzu haka ana cigaba da sasantawa tsakanin Villa din da golan,kuma ana saran nan da sa'o'i ashirin da hudu za a kamalla yarjejeniyar.

Tsohon golan Newcastle United da Blackburn Rovers ya samu kanshi a tsaka me wuya ne a City tun bayan da Roberto Mancini ya maida Joe Hart a matsayin golansa na farko.

Baya ga haka dai Villa na jiran sako daga Wigan Athletic akan Charles N'Zogbia wanda ta taya akan fan miliyon goma don ya maye gurbin Stewart Downing wanda ya koma Liverpool akan fan miliyon ashirin.