Manchester City na gabda sayen Aguero

aguero
Image caption Juventus da Real Madrid ma na zawarcin Sergio Aguero

Manchester City na gabda kulla yarjejeniya da dan kwallon Atletico Madrid Sergio Aguero,kamar yadda BBC ta fahimta.

Wannan matakin na zuwa ne duk da cewar akwai 'yan matsaloli akan batun sauya shekar Carlos Tevez zuwa kungiyar Corinthians ta Brazil.

City ta ce babu tantaba zata bige Juventus da Real Madrid a rige rigen sayen dan kwallon Argentina Aguero.

A baya Mancini yana jiran a kamalla yarjejeniyar sayarda Tevez kafin yayi yinkurin sayen Aguero.

Aguero ya bayyana kuru kuru cewar yanason barin Atletico kuma City na bugun kirji cewar sune zasu saye shi

Ya zira kwallaye 20 a gasar La Liga a kakar wasan data wuce tare da Atletico sannan yaci kwallaye 13 a cikin wasanni 30 daya bugawa Argentina.