Aston Villa ta sayi Given daga City

Image caption Shay Given

Aston Villa ta kammalan siyan mai tsaron gidan kasar jamhuriyar Ireland da kuma kungiyar Manchester City wato Shay Given.

Mai tsaron gidan wanda ke da shekarun haihuwa 35 ya sa hannu ne a yarjejeniyar da zai bugawa kungiyar Villa leda na tsawon shekaru biyar.

Sabon kocin kungiyar Alex McLeish ya sayi mai tsaron gidan ne bayan da Brad Friedel ya koma kungiyar Tottenham.

Given ya ce: "Aston Villa babbar kungiya ce, kuma ina matukar murnar zuwa kungiyar. zan yi duk mai yiwuwa domin ganin na cimma kowani irin kalubale da zan fuskanta a kungiyar."