Munason a siyo Luka Modric-Terry

Luka Modric Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luka Modric

Kyaftin din Chelsea John Terry ya ce sayen dan kwallon Tottenham Luka Modric babban kamu ne ga kulob din.

Modric mai shekaru 25 ana tunanin ya baiwa Spurs takardar bukatarsa ta barin kulob din bayan Blues sun bada tayin fan miliyon 27.

Terry yace"babban dan wasa ne da yake da dabarar murza leda".

Terry ya kara da cewar"siyoshi zuwa tawagarmu zai kara mana karfi".

Spurs ta gayama Modric wanda ya shafe watanni 14 cikin kwangilarsa ta shekaru shida cewar babu inda zashi.

Kyaftin din ya bayyana haka ne lokacin rangadin da Chelsea keyi zuwa nahiyar Asiya inda zasu buga wasa ta tawagar Malaysia.