Corinthians ta fasa siyan Tevez

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Carlos Tevez

Carlos Tevez dai baza bar kungiyar Manchester City ba domin komawa Corinthians saboda kungiyar ta fasa siyan dan wasan.

Da farko dai City ta amince da tayin fam miliyan 40 da Corithians ta yiwa dan wasan, bayan ya nunawa sha'awarsa na komawa taka leda a latin Amurka.

Amma har yanzu Corinthians bata fidda siyan dan wasan ba, mai shekarun haihuwa 27 a watan Junairu.

Manchester City da Corithians sun kasa cimma yarjejeniya ne akan dan wasan duk da cewa kuwa City ta amince da tayin da aka yi masa.