Chelsea ta bada tayi akan Lukaku na Anderlecht

Romelu Lukaku. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Romelu Lukaku

BBC ta fahimci cewar Chelsea ta bada tayi akan dan kwallon Anderlecht mai shekaru goma sha takwas Romelu Lukaku.

Kulob din na kasar Belgium na tattaunawa da Chelsea akan cinikin tun a watan daya wuce, duk da cewar matashin dan kwallon yana samun hari daga wajen Arsenal da Manchester City da kuma Tottenham.

A yanzu dai Blues din ta bada tayi me karfi akan dan wasan Belgium din, koda yake dai bayason nawa bane.

Lukaku ya zira kwallaye biyu a wasanni goman daya bugawa kasarsa.

A watan Yuni Janar Manaja na Anderlecht Herman van Holsbeeck ya ce "akwai nisa matuka akan sasantawa akan dan kwallon".