Hammam ya kalubanci binciken da ake masa

hammam
Image caption Mohammed Hammam

Tsohon dan takarar shugabancin Fifa wanda aka dakatar Mohammed Bin Hammam ya kalubalanci sahihancin binciken da ake yi akansa.

A ranukan Juma'a da Asabar ne kwamitin da'a na Fifa zai yanke hukunci akan batun zargin cin hanci akan dan kasar Qatar din.

Daga bisani Bin Hammam ya janye daga takarar bayan zargin sannan sai kuma aka dakatar dashi a ranar 29 ga watan Mayu.

Bin Hammam da tsohon mataimakin shugaban Fifa Jack Warner ana dakatar dasu ne saboda zargin sun yi kokarin sayen kuri'u don zaben Hammam a matsayin shugaban Fifa.

Zargin dai shine an bada dala dubu arba'in ga kungiyoyi 25 saboda zaben.