Everton taki amincewa da tayin Arsenal a kan Jagielka

jagielka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Phil Jagielka

Everton taki amincewa da tayin fan miliyon goma akan dan kwallonta Phil Jagielka daga wajen Arsenal.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya nuna sha'awarsa akan Jagielka mai shekaru 28 ne don samun wanda zai rike bayan Gunners ta tsakiya.

Idan har yanason cinikin ya kullu, tabbas sai ya bada kusan fan miliyon 20 kafin Everton ta amince.

Matakin Everton na kin yarda da wannan tayin, nada nasaba ba batun tayin fan miliyon 12 da Arsenal tayi a bara akan dan wasan.

Wenger ya dade yana zawarcin Jagielka tun lokacin daya bar Sheffield United ya koma Everton a shekara ta 2007.

Jagielka a watan Maris din data wuce ya sabunta kwangilarsa ta karin shekaru hudu a Everton kuma ana ganinsa a matsayin wanda zai maye gurbin Phil Neville a matsayin kyaftin din kulob din a nan gaba.