Dan Saliyo Strasser ya koma Lecce daga Milan

strasser Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rodney Strasser

Dan kwallon Saliyo Rodney Strasser ya koma kungiyar Lecce a matsayin aro na shekara guda daga AC Milan.

Dan wasan mai shekaru 21 ya shaidawa BBC tafiya aron yazo ne bayan ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyu da Milan din.

Strasser yace" Naji dadin wannan sauya shekar kuma ina saran zan samu damar bugawa a Lecce".

Strasser na cikin tawagar Milan data lashe gasar Serie A a kakar wasan data wuce, koda yake dai wasanni kadan ya buga.

Sannan kuma ya buga wasanni biyu ne kacal wa Milan a gasar zakarun Turai amma duka biyun daga benji ya taso.

A shekara ta 2007 ne Strasser ya shiga cikin tawagar matasan AC Milan kafin daga bisani ya koma babbar tawagar.

Strasser ya buga Saliyo wasanni hudu.