Carlos Tevez ya kudiri aniyar barin Manchester City

Image caption Carlos Tevez

Har yanzu dai Carlos Tevez na son barin kungiyar Manchester City, kuma bai damu da rushewar yarjejeniya tsakanin kungiyar da Corinthians ba, in ji wakilin dan wasan.

A ranar laraba ne kungiyar Corinthians ta ce ta fasa siyan Tevez saboda sun kasa cinmma matsaya da City kan dan wasan.

Corinthians dai ta taya Tevez ne akan fam miliyana arba'ain kuma City ta amince, amma kungiyoyin biyu dai sun kasa cimma matsaya kan yadda za'a biya kudin.

Wakilin Tevez, Kia Joorabchian ya shaidawa BBC cewa: "Carlos Tevez fa ake magana akai, daya daga cikin shahararrun 'yan wasan kwallon kafa a duniya, ko kadan bamu damu ba.

"Yana son ya bar City, amma har yanzu yana matsayin dan wasan City ne."

Joorabchian ya ce yana kyautata zaton wasu kungiyoyin za su zo neman dan wasan.