Park Ji-Sung ya sabunta kwantaraginsa da United

Image caption Park Ji-Sung

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce kungiyar ta kara wa'adin kwantaragin dan wasan Park Ji-Sung na tsawon shekaru biyu.

Kwantaragin Park, dai ya kamata ne ya kare a karshen shekarar 2012.

Ferguson ya ce: "Mu kara wa'adin kwantaraginsa, dan wasan na haskakawa sosai a kuniyar.

Park, ya zura kwallon a wasan sada zumuncin da Manchester ta doke Seatle Sounders da ci bakwai da nema.