'Liverpool za ta taka rawar gani' -Inji Rooney

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wayne Rooney

Dan wasan gaban Manchester United Wayne Rooney ya ce kungiyar Liverpool za ta taka rawar gani wajen lashe gasar Premier a kakar wasanni mai zuwa.

Liverpool, dai ta kammala kakkar wasan bara ne a matsayin ta shida, kuma a bana ta sayo wasu 'yan wasa kamar su Jordan Henderson da Charlie Adam da kuma Stewart Downing.

"A gaskiya sun siyo shahararun 'yan wasa." In ji Rooney.

"Na yi ammanar cewa za su kokari sosai domin ganin sun lashe gasar, kuma ina ganin za su iya hakan."

Rooney ya kara cewa kungiyoyin da ya ganin za suyi takarar lashe gasar da United, sun hada da Chelsea da Liverpool da Arsenal da kuma Manchester City.