Watakila in daina saka Balotelli-Mancini

balotelli Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Marion Balotelli

An cire dan kwallon Manchester City Mario Balotelli da wuri a wasan sada zumunci da LA Galaxy bayan manajansa yayi tunanin cewar, bai maida hankali ba akan wasan.

Dan wasan mai shekaru 20 yana gabda zira kwallo, sai ya juya baya ya nemi cin kwallon da dunduniya amma sai kwallon bai shiga raga ba.

Kocin City Roberto Mancini yace "ina saran hakan zai zama darasi".

Ya kara da cewar "Idan Balotelli ya maida hankali zai buga wasan minti 90, amma idan ba haka ba zai ci benci".

Bayan da aka cire Balotelli sai ya fito yanata maganganu ya kuma yarda goran ruwansa.

A watan Agustan ne Balotelli ya koma City daga Inter Milan akan fan miliyon 24, amma kuma yayi ta fama da rauni da kuma dakatarwa.

Ya zira kwallaye 10 cikin wasanni 28 amma kuma an bashi katin gargadi 11 da kuma jan kati sau biyu.