Ribery zai yi jinyar kwanaki hudu-Bayern

ribery
Image caption Franck Ribery

Watakila Franck Ribery ba zai buga wasan farko na bude gasar Bundesliga da Bayern Munich ba saboda rauni.

Dan kwallon Faransa din ya jimu ne a ranar Lahadi a gwiwarsa lokacin suna horo.

Sanarwar da Bayern ta fitar ta ce matsalar gwiwar Ribery baida tsauri kuma zai yi jinyar kwanaki uku zuwa hudu ne kawai.

Amma dai jaridar Bild ta bada rahoton cewar dan kwallon mai shekaru 28 ya turgude idon sawunsa na hagu kuma da yuwa ya buga wasan bude gasar tsakanin Bayern da Borussia Moenchengladbach a ranar bakwai ga watan Agusta.

Kuma dan wasan zia cigaba da jinya sai bayan kwanaki goma zai soma horo.