Na zo Barcelona ne in koyi kwallo-Sanchez

sanchez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alexis Sanchez

Dan kwallon Chile Alexis Sanchez ya ce yazo Barcelona ne don ya "koya daga wajen wadanda suka fi iyawa".

A ranar Litinin ne ya bayyana haka bayan sanya hannu a kwangilar shekaru biyar tare da zakarun Spain din.

Sanchez mai shekaru 22 ya ce akwai wadanda zamu koya daga wajensu kamarsu Messi da Xavi.

Kwangilar Sanchez da Barcelona yakai Euro miliyon 26 amma kuma akwai garabasar data kai Euro miliyon 11 da rabi idan har ya nuna kwazo.

Sanchez zai saka rigar kwallo mai lamba tara saboda tafiyar Bojan Krkic zuwa AS Roma.

Barcelona na kokarin karawa tawagarta karfi don kare kofin gasar La Liga dana zakarun Turai data lashe a kakar wasan data wuce.