Uruguay ta lashe gasar Copa America

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Diego Forlan da Luiz Saurez

Diego Forlan da Luis Suarez sun zura kwallaye a wasan karshe da Uruguay ta doke Paraguay da ci uku da nema a gasar Copa America.

Nasarar da Uruguay din ta samu shine na 15 a tarihi.

Suarez ne ya zura kwallo na biyu ana minti 12 da fara wasan, sannan Diego Forlan ya zura ta biyu, kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Forlan, wanda yake bugawa kasarshi wasa na 82 ya zura kwallo ta uku ne ana sauran minti guda kafin a tashi wasan.