Wigan ta amince da tayin N'Zogbia

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Charles N'Zogbia

Aston Villa da kuma Wigan Athletic sun cimma yarjejeniya tsakaninsu akan Charles N'Zogbia.

Dan wasan wanda dan asalin kasar Faransa ne kuma mai shekarun haihuwa 25, zai tattauna wasu sharudda da kungiyar ne, kafin a gama cimma yarjejeniya.

Kungiyar Aston Villa ta ce tana ganin, za'a kammala yarjejeniyar siyan dan wasan kafin karshen makon da muke ciki.

Babu daya daga cikin kungiyar da ta bayyana kudin da za'a siyar da dan wasan, amma rahotanni na nuni da cewa kudin zai kai fam miliyan tara da rabi.