Uefa:Messi da Ronaldo da Xavi na takara

messi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi

Xavi Hernandez, Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo na kokawa akan sabuwar kyautar da hukumar kwallon kafa ta Turai wato Uefa ta bullo da shi.

Sabuwar kyautar za a bada ne a ranar 25 ga watan Agusta.

Da dama na ganin cewar gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi ne zai samu kyautar duk da cewar Cristiano Ronaldo na Real Madrid ya zira kwallaye 40.

Sauran zaratan 'yan kwallon Turai:

Andres Iniesta - Barcelona - (Maki 33) Falcao - Porto - (Maki 17) Wayne Rooney - Manchester United (Maki 15) Nemanja Vidic - Manchester United (Maki 5) Zlatan Ibrahimovic - AC Milan (Maki 4) Gerard Pique - Barcelona (Maki 4) Manuel Neuer - Bayern Munich (Maki 3)