Chelsea ta bada aron Courtois zuwa Atletico

Thibaut Courtois Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Thibaut Courtois

Sabon golan da Chelsea ta siyo daga Genk Thibaut Courtois ya koma Atletico Madrid a matsayin aro.

Courtois mai shekaru 19 ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da Chelsea a farkon wannan watan.

Courtois ya taka rawar gani a kakar wasan data wuce a gasar Belgium abinda ya sanya kasar ta gayyace shi.

Dan wasan ya tafi aro ne a Atletico don maye gurbin David de Gea wanda ya koma Manchester United.