FIFA: Ivory Coast ce ta farko a Afrika

ivory coast
Image caption Tawagar 'yan kwallon Ivory coast

Har yanzu kasar Ivory Coast ta farko a fagen kwallon kafa a nahiyar Afrika kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta sanar a ranar Laraba.

Amma kuma bisa jerin Ivory Coast ce ta goma sha hudu a duniya sai kuma Masar wacce take ta biyu a Afrika sai Ghana ta uku a yayinda Burkina Faso take ta hudu sai Najeriya ta biyar.

Jerin na kasashen Afrika:

1.Ivory Coast 2.Masar 3.Ghana 4.Burkina Faso 5.Najeriya 6.Senegal 7.Afrika ta Kudu 8.Kamaru 9.Algeria 10. Tunisia

Jerin manyan kasashen a duniya:

1 Spain 2 Netherlands 3 Jamus 4 Brazil 5 Uruguay 6 Ingila