Aguero ya kamalla yarjejeniya da Man City

aguero Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sergio Aguero

Sergio Aguero ya kamalla kulla yarjejeniyar shekaru biyar tare da Manchester City daga Atletico Madrid.

Dan kasar Argentina din mai shekaru 23 a ranar Laraba ne ya isa Ingila don kamalla kwangilar akan fan miliyon talatin da takwas.

A ranar Alhamis da yamma City ta bayyana cewar an kamalla kwangilar kuma Aguero zai saka rigar kwallo mai lamba 16.

Kulob din ya ce dan kwallon watakila zai buga wasan a karshen mako.

Tun da farko Aguero ya rubuta a shafinsa na Tweeter cewar"Ni dan kwallon City ne kuma naji dadin kasancewa da kulob din".

Aguero ya shiga gaban Robinho a matsayin dan kwallon mafi tsada a tarihin Manchester City.