Emmanuel Emmenike ya koma Spartak Moscow

emenike
Image caption Emmanuel Emenike

Dan kwallon Najeriya Emmanuel Emenike ya bar kungiyar Fenerbahce ta Turkiya ya koma Spartak Moscow ta Rasha.

Emenike mai shekaru 24 'yan sanda Turkiya sun yi mashi tambayoyi a watan daya gabata akan batun joge a wasa.

A halin yanzu dai Fenerbahce na fuskantar barazanar kwace mata kofin gasar 2011 a yayinda ake cigaba da bincike akan saida wasa a lokacin gasar kwallon kasar a kakar wasan data wuce.

Ita kuma Spartak Moscow itace ta biyar akan tebur na gasar Rasha.

Emenike yayi sunane a Turkiya a kulob din Karab├╝kspor kuma yana cikin tawagar Najeriya da zata kara da Ghana a wasan sada zumunci a wata mai zuwa.