Fifa:Watakila a soma da na'urar fasaha a 2012

goal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An hana kwallon da Lampard ya zira a ragar Jamus

Watakila a soma amfani da na'urar fasaha don tantance shigar kwallo a raga lokacin gasar premier ta Ingila a kakar wasa ta 2012-13.

Hukumar dake tsara dokokin kwallon kafa zata yanke hukunci akai a watan Maris na 2012.

Idan har hukumar ta amince da hakan, shugaban Fifa Sepp Blatter ya ce gasar kasashe zasu iya amfani da na'urar a kakar wasa ta 2012-13.

Shugaban gasar premier ta Ingila Richard Scudamore ya ce da zarar an amince zasu fara amfani dashi.

Blatter ya kara da cewar wata kila ayi amfani da na'urar a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014 a Brazil.